23 Yuni 2020 - 03:41
Rikicin Ya Barke A CIkin Jam’iyyar APC Mai Mulki A Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC cewa ba da jimawa ba za a warare sabanin da ya kunno kai a cikin jam’iyyar.

(ABNA24.com)  Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC cewa ba da jimawa ba za a warare sabanin da ya kunno kai a cikin jam’iyyar.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta APC, Atiku Bagudu ne ya shaidawa manema labaru haka jim kadan bayan ganawarsa da shugaban Buhari a fadar Aso Rock Villa da ke birnin Abuja.

Bagudu wanda shi ne gwamnan jahar Kebbi, ya ce; Bayan da shugaban kasar ta Najeriya ya saurari jawabansu, ya yi musu alkawalin warware rikicin da ya kunno kai a cikin jam’iyyar ba da jimawa ba.

Gwamnan ya kara da cewa; Dalilin ziyararmu shi ne tattaunawa da shugaban kasa akan batutuwan da su ka shafi jam’iyyarmu, da kuma hanyoyin da za a warware sabani a jam’iyyar.

A cikin kwanakin nan dai rikicin shugabanci ya kunno kai a cikin jam’iyyar ta APC, bayan da wata kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole.



/129